ABNA24 : Alkalumman da ma’aikatar cikin gidan faransar ta fitar sun ce an samu mutane sama da dubu hamsin da suka shiga zanga zangar, daga cikin 5,000 sun kasance ne a birnin Paris.
Saidai zanga-zangar ta rikide a wasu sassan kasar inda arangama ta barke tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zangar.
Rahotanni daga kasar sun ce an farma wa manyan shaguna da dukiyoyin jama'a da bankuna, yayin da aka kona motoci da dama.
Masu zanga-zangar sun yi ta jifan yan Sanda da duwatsu, yayin da su kuma suke harba musu hayaki mai sa hawaye.
342/